Akwai buƙatar shugabannin Arewa su ceto yankin daga durƙusshewa--Tsohon Shugaban ƙasa
Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya janaral Ibrahim Badamasi Babangida ya nemi shugabannin Arewa da su ceto yankin daga durƙushewa, a wani jawabin daya gudanar da Asubahin yau.
Babangida yace "Kunga dai duk manyan dattawan yankin suna ta faɗuwa suna mutuwa tun daga manyan malaman addinin siyasa da dai sauran su, nima kaina ina ji a jikina daƙyar idan wannan wannan shekarar zata fita ban koma ga Allah ba, fatanmu dai shi ne cikawa da imani".
"Saboda haka ina kira ga shugabannin wannan yanki namu, na arewa, mu dai lokacin da muke da dama mun yi iya abinda za mu iya, da ace na bar babban birnin tarayya a jihar Legas, ban dawo da shi yankina na arewa ba to da yanzu ba'a ma san inda arewar take ba, Alhamdu Lillahi mun yi iya abinda zamu iya yanzu mu tamu tazo ƙarshe don Allah shugabannin arewa ku haɗa kan ku ku ƙwaci yankin nan namu domin bamu da kamar sa".
In ji shi kamar yadda ya bayyana a jawabin nasa.
managarciya