Matsalar tsaro nafin karfin Gwamnatin tarayya - Kwankwaso 

Matsalar tsaro nafin karfin Gwamnatin tarayya - Kwankwaso 

Jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a Najeriya, yana mai gargadin cewa alamu na nuna matsalar na neman ta fi ƙarfin Gwamnatin Tarayya.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X da Facebook, tsohon Gwamnan Kano ya yi nuni da cewa matsalar tsaro da ake fuskanta a yanzu na iya zama babbar barazana ga haɗin kai da zaman lafiya a ƙasar.

Kwankwaso ya ce yadda gwamnati ke barin jihohi su kafa ƙungiyoyin tsaro na ’yan sa kai ba tare da isasshen horo ba, na nuna rauni a tsarin tsaro, lamarin da ya janyo yawaitar faɗaɗa makamai a faɗin ƙasa.

“Dukkan alamu na nuna cewa rashin tsaro na neman ya fi ƙarfin gwamnati. Wannan na bayyana a yadda ake barin jihohi su kafa ƙungiyoyin ’yan sa kai ba tare da horo na musamman ba. Wannan mataki, ko da an yi shi da kyakkyawar niyya, ya haifar da yaɗuwar ƙananan makamai da manyan makamai a ƙasar,” in ji shi.

Ya kuma bayyana damuwa kan karuwar tsangwama, azabtarwa da cin zarafin ’yan Najeriya, musamman daga wasu yankuna, tare da zargin cewa wasu ’yan siyasa na amfani da kalaman ƙiyayya a kafafen sada zumunta don rura wutar rikici da rarrabuwar kai.

Kwankwaso ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa domin dakile yaduwar rikice-rikice kafin abubuwa su ƙara tabarbarewa.

Haka kuma, tsohon Gwamnan ya taya sabon Ministan tsaro, Christopher Gwabin Musa murna bisa nadin da aka yi masa inda ya bayyana fatan cewa, Ministan zai kawo sauyi a fannin tsaro.