Ambaliyar Ruwa: Tinubu ya umarci Kashim Shettima ya garzaya zuwa birnin Maiduguri
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettim ya aika sakon jaje na shugaban kasa Tinubu ga dukkan wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.
Shettima ya aika sakon shugaban kasar ne a yayin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki kan fanni kudi da bankuna a Abuja.
Mataimakin shugaban kasar yayi amfani da taron wajen jajantawa 'yan Nijeriya da ambaliyar ruwa ya shafa a fadin kasar.
"Bayan wannan taron, bisa umarnin shugaban kasa, zan tafi Maiduguri cikin gaggawa inda ambaliyar ruwa ta afku.
" Ba iya bangare daya abun ya shafa ba. Muna fuskantar wannan kalubale daga Bayelsa har zuwa Sokoto.
"Ina tabbatar da cewa, shugaban kasa yana sane da abubuwan dake damun kasar nan kuma zai yi duk mai yiwuwa wajen kawo gyara", inji Shettima.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa mutane da dama ne suka rasa muhallinsu bayan ballewar dam din Alau dake Maiduguri.
managarciya