Kasa da Awa 24 da Daura Aurensa, Ango Yabar Duniya A Sakkwato 

Kasa da Awa 24 da Daura Aurensa, Ango Yabar Duniya A Sakkwato 

 

Wani matashi mai suna Shehu Lili dake unguwar  Kofar Atiku ya rasa ransa kasa da sa’o’i 24 bayan daurin aurensa da masoyiyarsa a jihar Sokoto. 

Wani dan uwan iyalan, Shamsudeen Buratai wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin yace Lili ya rasu ne bayan rashin lafiyar farat daya, shafin LIB suka rahoto. 
Kamar yadda Buratai yace, an daura auren angon wurin karfe 5 na yammacin Lahadi, 30 ga watan Oktoban 2022 a kofar Atiku dake Sokoto kuma yace ga garinku da safiyar Litinin. 
“Shehu abokina ne tun muna yara kuma abokai gidajenmu suke sama da shekaru 30. 
Ya samu cutar zazzabin cizon sauro ne wacce ke kayar da shi duk sanyi. 
Kamar kowacce shekara, ciwon ya taso shekarar nan wurin Satumba wanda ya sha magani kuma ya samu lafiya.” 
“A safiyar yau wurin karfe 9 na safe Shehu ya fito kuma ya same su har muka gaisa. 
Babu dadewa sai ya fara jin wani iri kuma yace mana ya tsammanin cutar da ce take son dawowa. 

Abu na gaba shi ne faruwar Shehu wanda daga nan kuma bai tashi ba.”  Shamsu yace. 
Tuni dai aka birni marigayin angon kamar yadda addini ya tanadar.