Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto shugaban kwamitin tsaro na Majalisar Dattawa ta kasa kana mamba a kwamitin Ilimi na Majalisar ya Samar da wata Makarantar karatun ilmin Furamare da karamar sakandare da za ta kula da karatun Masu lalura ta musamman da kuma Masu lafiya.
Wannan aikin Makarantar dai Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman ne ya samota ga hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa wato UBEC.
Da yake zagaya damu a sassan Makarantar dake kan titin Mai tuta a cikin Wani Sashen Makarantar Sarkin Musulmi Abubakar wato SAC, Darektan Lamurran Mulki na ofishin Sanata Wamakko Alhaji Almustapha Abubakar Alkali ya bayyana cewa, Makarantar ita ce ta karshe da aka bayar a duk fadin kasar nan, amma kuma ta kasance ta farko da aka fara kammala ginin ta.
Ya kara da cewa Wannan kuwa bai rasa nasaba da irin jajercewar Maigirma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kan sha'awar sa a fannin ilimi.
Almustapha Alkali ya bayyana cewa, a cikin Makarantar an tanadi, Ajujuwan karatu sama da Ashirin, ofisoshin malamai na Sashen Naziri, Furamare da karamar sakandare, kana an tanadi Babban dakin saukar da Baki da sama da makewayai Hamsin da wadatattun ruwan sha da na'urar bada hasken lantarki Mai karfin Doki Dari biyar da dakin injimin Samar da wutar wucen gadi ko ba wuta.
Ya kara da bayanin cewa an kewayen Makarantar da ingantaccen Bango da wayar Samar da tsaro da saka itatuwa domin kariya ga Hamada.
Alkali ya ce nan bada jimawa ba za a saka dukkan kayan karantawar da ake bukata domin Buda Makarantar da kuma soma karatu a cikinta.
Almustapha Abubakar Alkali ya ci gaba da cewa, an tanadi dakunan koyon karatu na zamani ga Masu fama da lalura kamar Studio, E-Library da sauran dakunan nazarce-Nazarce ga Daliban.
Alkali, ya bayyana Sanata Wamakko a mastayin gwarzo Mai kaunar ilimin diyan talakkawa a Jihar Sokoto.
Ya yi Kira ga sauran wadanda aka zaba da su yi koyi da Sanata Wamakko kan ciyar da mazabun su a gaba.
Daga nan sai ya yi Kira ga gwamnatin Jihar sakkwato da ta yi kokari kawo kwararrun malaman da zasu kula da Makarantar a duk lokacin da za a Buda Makarantar domin cimma manufar da aka Sanya a gaba.
Shima da yake tofa albarkacin Bakin sa, Wani Masanin Ilimi kana tsohon sakataren zartarwar hukumar ilimin Larabci da Addinin musulunci na Jihar sakkwato Alhaji Ahmad Baba Altine, ya jinjinawa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kan samo aikin Makarantar ga Gwamnatin tarayya.
Ya bayyaya cewa, abinda ya rage shi ne gwamnatin ta Maida hankali ga kula da Makarantar domin cimma manufar Gina ta.
A Halin da ake ciki dai yanzu an Riga an kammala aikin Makarantar Mai suna UBEC SMART SCHOOL, SOKOTO, abinda ya rage shi ne saka kayan aiki da kuma soma aikin karantarwa ga Makarantar.
Labari: Bashar Abubakar, Mataimaki na Musamman ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kan kafar watsa labarai ta zamani.