DHQ Ta Yi Martani kan Batun Kwace Motocin Sojoji da 'Yan Bindiga Suka Yi a Zamfara 

DHQ Ta Yi Martani kan Batun Kwace Motocin Sojoji da 'Yan Bindiga Suka Yi a Zamfara 

Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta musanta cewa cewa ƴan bindiga sun ƙwace motoci masu sulke guda biyu na sojoji a jihar Zamfara. DHQ ta kuma musanta iƙirarin cewa an hallaka mutane masu yawa waɗanda ƴan ta'adda suka binne tare da rahotannin sace mutum 150 a Sokoto. 
Martanin na DHQ na zuwa ne bayan wasu bidiyoyi sun yaɗu wanda suke nuna ƴan bindiga na murnar ƙwace motocin sojojin, cewar rahoton jaridar The Punch. 
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana bidiyoyin a matsayin na ƙarya, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da zancen.
Da yake bayani kan abin da ya faru a Zamfara, Edward Buba ya bayyana cewa motocin sun maƙale ne a cikin taɓo yayin da suke ƙoƙarin farmakar ƴan bindigan a ƙauyen Kwashabawa. Ya ƙara da cewa dakarun sojojin sun cire kayayykin da ke da amfani a cikin motocin domin hana ƴan bindigan yin amfani da su. Manjo Janar Edward Buba ya kuma bayyana cewa bidiyon da aka yaɗa wanda ya nuna ƴan ta'adda na binne mutane masu yawa ba a ƙasar nan ya faru ba.