Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Kuma Shugaban Majalisar koli ta Harakokin Addinin Musulunci Na Najeriya, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya jawo hankalin al'ummar musulmi kan bukatar da ake da ita na su tashi tsaye wurin yi wa kasar Nijeriya addu'a.
Yayi Kira ga al'ummar wannan kasa da su tashi tsaye wurin gudanar da addu'o'in neman samun zaman lafiya ga wannan kasa a kan halinda ake ciki na rashin tsaro
Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar ya yi kalaman ne a lokacin da ya halarci bukin yaye dalibai 168, karo na hudu a makarantar Sheikh Dahiru Usuman Bauchi dake jihar Sakkwato wadanda suka haddace alkur'ani Mai girma.
Kwamishinan Ma'aikatar lamuran Addini Honarabul Abdullahi Maigwandu ( Marafan Wazirin Sakkwato) wanda shi ne ya wakilci Gwamna Tambuwal a wurin taron, ya ba da tabbacin wannan gwamnati shirye take wurin ba da gudunmawa ta kowane bangare domin karfafa sha'anin addinin musulunci.
Ya kuma ba da tabbacin zai isarda Sakon Shugabannin wannan makaranta ga maigirma gwamna, domin Samarda hilin da wannan Makaranta za ta gina ajuzuwan karatu.
Daga cikin muhimman mutane da sunka shedi wannan bukin akwai Khalafah Sheikh Dahiru Usuman Bauchi, da kuma alarammomi da manyan Shehinnan Darikar Tujjaniya dake cikin wannan kasa da wajenta.