An tsaurara tsaro yayin da za a yi zaɓen gwamna a Osun

An tsaurara tsaro yayin da za a yi zaɓen gwamna a Osun

An jibge da kuma baza jami’an tsaro sosai a garin Osogbo, babban birnin Jihar Osun, yayin da jihar ke shirye-shiryen ƙarshe na zaɓen gwamna da za a gudanar a gobe Asabar.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN da ya zagaya garin a yau Juma’a ya ruwaito cewa an ga ƴan sandan Najeriya an jibge su a muhimman wurare.

Hakazalika an ga motocin yaƙi, ɗauke da makamai na sojoji suna sintiri a cikin garin.

An kuma ga jami’an hukumar tsaron fararwn hula ta Najeriya, NSCDC a wurare daban-daban.

Hakazalika an ga jami’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa, FRSC a wurare masu muhimmanci da ke kula da zirga-zirgar ababan hawa a cikin garin da kuma wajensa.

Ofishin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, dake kan titin Gbongan/Osogbo ma cike ya ke da dimbin jami’an tsaro.

Idan dai za a iya tunawa babban sifeton ƴan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba ya ce za a tura jami’an ‘yan sanda 21,000 domin gudanar da zaben gwamna a jihar.