Obasanjo Ya Bukaci Tinubu Ya Kori Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa

Obasanjo Ya Bukaci Tinubu Ya Kori Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa
 
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira da a kori shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu. 
Obasanjo ya ce ya kamata a kori jami’an INEC a dukkanin matakai a wani bangare na sake fasalin tsarin zabe a Najeriya. 
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana a wani taron shugabanci na gidauniyar Chinua Achebe a Jami’ar Yale, da ke Amurka, inji rahoton Premium Times. 
Yayin da ya nemi a gaggauta tsige Farfesa Mahmood, Obasanjo ya bayyana zaben 2023 a matsayin “wani abu da ya saba hankali.” 
 
Tsohon shugaban na Najeriya ya ce dole ne shugaban hukumar ta INEC ya zama ya fi karfin masu mulki kuma ya kasance wanda ba za a iya juya shi da cin hanci ba. 
Obasanjo ya ce abin takaici ne yadda shugaban INEC din da kansa ya kawo tsarin amfani da fasahohin BVAS da IREV amma a karshe basu yi amfani ba. 
Ya zargi INEC da kin yin amfani da na'urorin a yayin zaben 2023 wanda ya jawo aka samu kura kurai a zaben, lamarin da ya kira 'kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.' 
Obasanjo ya kuma yi kira da a rage wa jami’an INEC wa’adi da kuma tsaurara matakan tantancewa domin hana nada ‘yan bangar siyasa.