Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya sauyawa manyan sakatarori shida wurin aiki.
Tambuwal ya yi bazata a sauyawa wurare musamman ɗaya daga cikinsu da yake makusanci gare shi waton Faruku Shehu da yake a hukumar bayar da ilmin furamare ta jiha zai koma ofishin shugaban ma'aikata don jiran sabon wurin aiki.
1. Abubakar Usman Junaidu - Babban Sakatare a Protocol
2. Abdullahi Saidu Bafarawa- Babban sakatare a ma'aikatar jindaɗi da walwala
3. Abubakar Yusuf Sanyinna - Babban sakatare a ma'aikatar addini
4. Abubabar Haliru Dikko - Babban Sakatare a ma'aikatar ayukka da sufuri.
5. Ahmed Rufai Ibrahim-Babban sakatare a hukunar bayar da ilmin furamare ta jiha (SUBEB)
A takardar da shugaban ma'aikatan jiha Alhaji Abubakar Muhammad ya sanyawa hannu ta bayyana sauye-sauyen..