Gwamna Zamfara Ya Rage Ma'aikatun Jihar  Daga 28 Zuwa 16 

Gwamna Zamfara Ya Rage Ma'aikatun Jihar  Daga 28 Zuwa 16 

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya rattaɓa hannu kan dokar zartarwa wacce ta rage yawan ma'aikatun jihar daga 28 sun koma 16 kaɗai. Gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin sauya akalar ɓangaren aiki ya koma kan turbar amfani wanda al'umma zasu san ana shugabantarsu, a cewar rahoton Leadership. 

Dauda Lawal ya ƙara da cewa garambawul din da aka ga yana yi a gwamnatin Zamfara na cikin kudirinsa na rage kashe-kashen kuɗi na ba gaira ba dalili.
Ya ce wannan matakin na daga cikin aniyarsa ta zakulo muƙarrabai na gari waɗan da zasu shayar da mutanen jihar Zamfara romon demokuraɗiyya. 
"A wani ɓangaren yunkurin gwamnatina na canja sashin ayyuka ya zama mai amfani kuma ya riƙa aikin da aka buƙata, na sa hannu kan dokar rage yawan adadin ma'aikatu daga 28 yanzu sun koma 16." "Na yi wannan ne ba don komai ba sai don cika burina na zakulo haziƙan mukarrabai, waɗanda zasu rage yawan kashe-kashen kuɗi kuma su zuba wa al'umma romon demokuraɗiyya."