Daliban Makarantar Sakandiren Yauri 30 Sun Kuɓuta Daga Hannun Masu Garkuwa Da Su

Rahotanni daga jihar Kebbi na nuna cewar akalla daliban makarantar Sakandiren Gwamnatin tarayya dake Yauri talatin ne suka kubuta daga hannun masu garkuwa da su.

Dalibban Yauri

Wata majiya mai tushe ta shaida mana cewar yanzu haka daliban na gidan Gwamnatin jihar Kebbi inda aka basu abinci da ruwa. Nan gaba a yau ne Gwamnan jihar Atiku Abubakar Bagudu zai yi taron manema labarai domin gabatar da daliban guda 30 da aka kubutar.