Jirgin ruwa ya kife da mutane 40 a Sakkwato

Jirgin ruwa ya kife da mutane 40 a Sakkwato

 

Jirgin ruwa ya kife da mutane 40 a gulbin da ke garin  Dundaye cikin karamar hukumar Wamakko a jihar Sakkwato.

Jirgin na katako ya kife ne sakamakon ruwan da suka yi ambaliya suna gudu da karfi a gulbin na Dundaye.
 
Ayuba Maya Dundaye a gabansa lamarin ya faru ya tabbatar wa wakilinmu cewa mafiyawan mutanen da jirgin ya dauko mata da ƙananan yara ne za su tafi gona  suke son su tsallaka gulbin lamarin ya faru da su.
Ayuba Maya ya kara da cewar jirgin ruwan na katako  dauke da fasinjan ya kai tsakiyar gulbin ya nutse, nan take masu fito da suka iya ruwa a kauyen suka ceto mutane 15 yayin da mutane 25 ba a gansu ba  har zuwa lokacin hada rahoton.
Maya ya ce a lokacin da lamarin ke faruwa wakilin uban kasa ne kawai wurin domin ganin an ceto mutane.
Mai ba da shawara ga Gwamnan Sakkwato kan ba da agajin gaggawa Nasir Garba Kalambaina ya ce bai san da faruwar lamarin ba a lokacin da aka tuntube shi amma zai tura jami'ansa ya kuma sanar da hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa don tura ma'aikata in da lamarin ya faru. 
Garba Kalambaina ya ce da ikon Allah jami'ansa za su tabbatar da ceto wadanda suka nutse a ruwan.
Sanata Aliyu Maggatakarda Wamakko ya jajantawa iyalan mutanen da suka kife a jirgin a garin Dundaye ya nuna kaduwarsa ga samun labarin abin da ya faru ya ce abu ne daga Allah.
Maitaimakawa Sanata a bangaren yada labarai Bashar Abubakar a bayanin da ya fitar ya ce ya roki Allah wadanda suka rasu Allah ya garta masu wadan da aka ceto kuma Allah ya ba su lafiya.