Gwamna Sakkwato ya raba Keken Guragu 500 ga masu lalura ta musamman a jiha

Gwamna Sakkwato ya raba Keken Guragu 500 ga masu lalura ta musamman a jiha
 
 
 
Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu ya  kaddamar da rabon kekunan guragu guda 500 ga masu bukata ta musamman a jihar Sakkwato, a wani bangare na ranar masu bukata ta musamman ta duniya. 
Gwamnan ya ce manufar wannan mataki shi ne tallafawa al'uma masu bukata ta musamman tare da tabbatar da cewa sun cigaba da morar gwamnati.
 
"Hakan na cikin tsarin mu na tabbatar da cewa kowanne bangare na al'umma ya amfana da shirye-shiryen gwamnati.
 
"Domin tabbatar da cewa an samar wa masu bukata ta musamman cigaba mai dorewa a wannan jiha tamu, mun yi tanadi a kasafin kudin shekarar 2025 domin gyara makarantar masu bukata ta musamman ta A.A Raji domin bunkasa ilimin su.
 
"Mun kuma yanke shawarar kara adadin wadanda ke amfana da alawus din wata-wata da muke bawa mutane 6,679 zuwa mutane 10,000 tare da fara shirye-shiryen raba kekunan guragu kashi na biyu domin cigaba da inganta rayuwar masu bukata ta musamman a jihar Sokoto.
 
"Gwamnati na amfani da wannan dama domin godewa tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma sanata mai wakiltar Sakkwato ta Arewa Sanata  Aliyu Magatakarda Wamakko bisa tallafin N10,000 da ya bawa masu bukata ta musamman guda 6,679 domin wannan rana.
 
"Za mu cigaba da jajircewa wajen inganta rayuwar al'umar wannan jiha a kowanne mataki," kalaman Gwamnan Sakkwato.