Shugaba Buhari ya bayyana kudirinsa kan 2023

"Matsalar da ta tsaya min a rai ita ce arewa maso yamma ana kashe mutane da sace wa a ko'ina, abu ne da ake cikin mawuyacin hali, za mu cigaba da aiki sosai har mun mayar da doka da oda", a cewarsa Shugaba Buhari ya roki 'yan Nijeriya dake zaune a can  su cigaba da biyar doka da oda, in suka yi haka ba abin da zai kawo masu cikas kan fahimtar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Buhari ya bayyana kudirinsa kan 2023

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai bar ofis a 29 ga watan Mayun 2023 ya gargadi masu yi masa yekuwar kara wa'adin mulki.

"na rantse da al'kur'ani zan yi mulki kamar yadda kundin doka ya tanadar, zan wuce in wa'adi ya cika, ba Tazzarce bana son na ji wani ya fara zancen gyaran kundin tsarin mulki don a kara min wa'adi, ba zan aminta da hakan ba."

Ya sanar da hakan ne lokacin da yake tattaunawa da 'yan Nijeriya dake zaune a Saudi Arebiya bayan ya kammala ziyararsa.

Ya ba da tabbacin a cikin watanni 18 da saka rage masa zai kara kokarin inganta rayuwar mutanen kasa, don samun cigaban Nijeriya.
Ya yi amfani da damar wurin kiran mutanen kasa su rika yiwa gwamnatinsa adalci a kowane lokaci, ya roki masu suka da su kwatanta yanayin tsaro a Arewa maso gabas da Kudu maso kudu a 2015 da yanzu an samu cigaba.
"Matsalar da ta tsaya min a rai ita ce arewa maso yamma ana kashe mutane da sace wa a ko'ina, abu ne da ake cikin mawuyacin hali, za mu cigaba da aiki sosai har mun mayar da doka da oda", a cewarsa

Shugaba Buhari ya roki 'yan Nijeriya dake zaune a can  su cigaba da biyar doka da oda, in suka yi haka ba abin da zai kawo masu cikas kan fahimtar dake tsakanin kasashen biyu.