A Shekara Ɗaya Amadun Alu Ya Mayarda Sakkwato Sabuwa----Abba Shehu Tambuwal

 A Shekara Ɗaya Amadun Alu Ya Mayarda Sakkwato Sabuwa----Abba Shehu Tambuwal

Ɗaya daga cikin jigogin tafiyar gwamnatin jihar Sokoto da ke faɗi tashin ganin an samar da cigaba a jiha Alhaji Abba Shehu Tambuwal ya bayyana yadda aka samu gagarumin sauyi a cikin shekara ɗaya bayan da Gwamna jiha Dakta Ahmad Aliyu ya karɓi ragamar jagoranci.

Alhaji Abba Tambuwal yana cikin aminan gwamnatin jihar Sokoto da ba su da buri sai samar da  romon dimukuraɗiyya mai ɗorewa a tsakanin matasan jiha,  ya ce bai yi mamakin yanda aka samu gagarumar cigaba a cikin lokaci kaɗan ba, domin saninsa da Maigirma Gwamna mutum ne da yake da jajircewa da kishin Sakkwato.

"Ina yi wa Allah godiya ganin yanda ya ƙarfafa Gwamna Amadun Alu bai ba mu kunya ba, muna alfahari da shi da gwamnatinsa, yanda take sauraren jama'a da ƙoƙarin kawo masu cigaba.

"Muna da yaƙinin ƙudurorin Gwamna guda 9 za a cimma nasara kansu yanda matasa maza da mata da tsofaffi da manoma da 'yan kasuwa mutane birni da ƙauye za su ci gaba da cewa 'Sakkwato sai Amadun Alu' domin a yau ana saman turba mai kyau," Kalaman Abba Tambuwal.

Ya zayyano wasu ƙoƙari da Gwamnan ya yi a wannan ƙaramin lokacin kamar cigaba da biyan albashin ma'aikata kan kari a kowane wata da dawo da kuɗin tafiyar da ma'aikatu da aka bari a gwamnatin da ta gabata, fara biyan kuɗin garatitu a cikin bashin biliyan 14 da ya gada ga gwamnatin baya tun daga 2015-2023, wannan biyan zai taimakawa tattalin arzikin jiha, gwamnati ta sayo babura 1000 da Agwagwa da buje 500 domin fara rabawa matasa su yi dogaro da kansu, an samar da hanyoyin mota sun fi 50, an gyara matsalar ruwan sha a jihar Sakkwato, ba wani gefen al'umma da gwamnatin ba ta yi wani hovvasa ba musamman yanda ta himmatu wurin farfaɗowa da ilmin furamare.