Rudu A Jam’iyar PDP:Ana Yunkurin Hana Atiku, Tambuwal Da Saraki Tsayawa Takara

Rudu A Jam’iyar PDP:Ana Yunkurin Hana Atiku, Tambuwal Da Saraki Tsayawa Takara

Wani sabon rudu ya shigo jam’iyar PDP a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyar da aka gabatar jiya Talata abin da ya sanya aka dage zuwa yau Laraba.

Rikita-rikitar ta soma ne a lokacin da wasu jagorori a kudancin Nijeriya suka yi tsaye sai an hana duk wanda ya bar jam’iyar PDP ya sake dawowa tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Majiyar ta ce gwamnan da yafi kowane Magana ne a yanki ya yi wannan kiran.  Atiku Abubakar da Bukola Saraki da Aminu Waziri Tambuwal da Rabi’u Musa Kwankwaso tare da wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheka suka shiga jam’iyar APC a zaben 2015.

Sun sake dawowa PDP kan wasu dalilai na rashin fahimta da suka samu a can a yanzu dukkansu suna bukatar samun tikitin takara a PDP.

Masu ra’ayin a kar aba su dama sun ce sauya shekarsu tana cikin babban dalilin faduwar jam’iyar PDP in da ta koma jam’iyar adawa.

Wasu mambobi daga Arewa ba su yarda da wannan shawara ba sun ce ka da a kullaci kowa bai dace a yi kokarin ganin bayan wasu ba, “Duk wanda yake kiran a dakatar da wasu saboda mi za a yi haka”.

Rashin fahimtar ta sanya shugaban jam’iya Dakta Ayu rufe zaman zuwa yau(Laraba).

Mai Magana da yawun PDP Debo Ologungba ya ce an dauki matakin dakatar da zaman ne domin abaiwa saura kwamitocin da aka nada damar duba rahotonsu su gabatar wa majalisar zartarwar jam’iya domin amincewa.

Chief Raymond ya tabbatar da rashin fahimtar da aka samu a kokarin hana wasu takara, ya ce wannan abu ne kokarin raba jam’iya.