Tafiyar Mu Ta Girmama Mutanen Sakkwato Da Samar Musu Cigaba Ce---Sanata Wamakko

Tafiyar Mu Ta Girmama Mutanen Sakkwato Da Samar Musu Cigaba Ce---Sanata Wamakko
Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana yadda tsarin tafiyarsu ta siyasa yake ga mutane wanda ba'a samu a sauran jam'iyyu ba musamman a PDP waton girmamawa da samar da cigaba a jiha.
Sanata Wamakko a lokacin yekuwar zabe a karamar hukumar Tangaza a ranar Jumu'a ya ce tafiyar mu ta girmama mutanen Sakkwato da samar musu cigaba ce.
"Jama'ar jihar Sakkwato ana siyasa domin cigaba da amfana abin da babu a jam'iyar PDP, shekara takwas a Sakkwato babu cigaba in kuka zabi Amadu za ku sha miya da Guraye.
"Sanin kowane a lokacin jagorancnin Alu ma'aikaci da mata da matasa da 'yan kasuwa sun amfana sun samu walwala," kalaman tsohon Gwamnan Sakkwato Sanata Aliyu Wammako.
Ya yi alkwalin zai gyara wutar Tangaza da ta samu matsala taswon lokaci gwamnatin jiha ta PDP ta fita batun mutane a cikin duhu.
Sanata Wamakko ya jawo hankalin mutanen jiha ga zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyar APC Bola Ahmad Tinubu domin shi mutum ne mai son Arewa da Nijeriya, "a cikin ikon Allah a 2014 shi ne ya sa aka kawo APC ya ba  da tashi gudunmuwa domin dimukuradiyya da kasa su cigaba, yana da kwarewar da zai kawo sauyi mai alfanu a kasar nan don haka a ba shi goyon baya," a cewar Sanata Wamakko.
Dan takarar Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto a jawabinsa ya sanar da gyran fuska da ya yi wa kudurorinsa Takwas in da suka koma guda Tara a yanzu, ya kara da inganta harkokin addini, dudu ba da yanda ake bukatar inganatar da shi a jiha.
Ahmad Aliyu ya ce siyasar da ake yi a yanzu ba Alu ko Amadu ake yi wa ba, abu ne na neman mafita domin PDP ta kasa lokaci ya yi da za ta kwashe kayanta a Sakkwato, ta bar gidan haya mulkin kama karya ya zai gushe.  
 
A karamar hukumar Gudu dan takarar Gwamna ya yi masu alkwalin zai samar da Sikandare   da gyaran babban hanyar Gudu da kammala hanyar  Balle zuwa Bachaka.
Ya ce mutane suna shakku in an yi masu alkawali don an yi ta yi ba cika ba wannan ba irin nasu ba ne.
"Muna son ku tambayi mutanen PDP mi suke maku a Gudu in ba su yi ba, ba  dalilin zabensu, kar ku zabe su.
"Mun yi maku alkawalin Ahmad Aliyu zai biya maku bukatunku na ruwan sha  da sauran abubuwa kamar yadda Sanata Aliyu ya yi maku," a cewarsa.