Sakkwato An Samu Sauye-Sauye Masu Amfani a Mulkin Amadun Alu----Injiniya Aminu Ganda

Sakkwato An Samu Sauye-Sauye Masu Amfani a Mulkin Amadun Alu----Injiniya Aminu Ganda

Gwamnan jihar Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu a shekara ɗaya yana kan mulkin jihar Sakkwato ya yi ƙoƙari sosai, aikin da yake yi ba sai an faɗi ba a zahiri kowa na ganinsu sai godiyar Allah an samu Sauye-Sauye masu amfani da yawa tun daga kan ƙoƙarinsa na ƙawata birnin jiha da samar  da aiyukka da samo wasu aiyukka muhimmai daga gwamnatin tarayya.
Jigo a jam'iyar APC Injiniya Aminu Ganda ne ya faɗi haka a wata tattaunawa da Managarciya ya ce mutane sun ga ɗimbin aiyukkan da mai girma Gwamna ya aiwatar kan haka jagororin jam'iyar APC sun tabbatar da ƙoƙarin mai girma Gwamna musamman a wurin kawo aiyukkan gwamnatin tarayya yanzu haka ministan Albarkatun man fetur zai zo Sakkwato saboda gayyatar da Gwamna ya yi masa na ya zo a soma binciken Mai da Gas da ake da shi a jiha, in wannan ƙudirin nasa ya cika ya yi abin da ba wanda ya yi a gwamnonin Arewacin Nijeriya.
Aminu Ganda ya ce Gwamna ya yi hoɓɓasa a gefen makamashi da wutar lantarki in da ministan Wuta ya yi alƙawarin shiga cikin aikin samar da wuta mallakar jiha waton IPP, ga batun mayar da hasken wuta a yankin gabascin Sakkwato da suka shafe shekara 10 ba wutar lantarki ba ƙaramin cigaba ba ne.
Kan masu ƙorafi makusancin ga Gwamna ya ce "a kowace tafiya ba a cewa babu kuskure amma abin da ake so cigaba ya rinjaye akasinsa, akwai waɗanda duk abin da ka yi saboda hasada da adawa sai sun ga baka yi abin da yakamata ba, wasu kuma a tafiyar gwamnati ne aka ɗauki matakin da bai yi masu daɗi ba, sai ka samu suna ƙorafi, ƙarshen magana dai abin da ake son sani mafiyawan mutane sun amfana domin ko a jarabawa ba sai ka samu ɗari bisa ɗari ba, kashi 50 ka ci jarabawa, tun da mafiyawan mutanen Sakkwato sun amfana waɗanda aka saɓawa su yi haƙuri za su amfana a wannan tafiyar.
"Fatar mu Allah ya sa dafawa Amadu ya ƙare mulkin lafiya, kamar yadda ya soma," Kalaman Injiniya Aminu Ganda.