Rabon babura da shinkafa: Shin Sanata Wamakko ya yi abin da ya dace?

Rabon babura da shinkafa: Shin Sanata Wamakko ya yi abin da ya dace?
Tsohon Gwamnan Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya shirya raba babura 1000 da buhun shinkafa dubu 10 mai kilo gram 50 da injimin markade ga dukkan kananan hukumomi takwas da yake wakilta.
A matakin farko kananan hukumomi Silame da Tangaza da Binji da Gudu aka fara  rabawa kayan in da baburan 50 za su samu a kananan hukumomin, in da shugaban mazaba da shugabannin mata dana Social media da sarakuna za su cibgajiyar.
A karo na biyu kananan hukumomin Kware da Sakkwato ta kudu da Sakkwato ta Arewa da Wamakko za su amfana babur mai taya uku dake aiki da wutar lantarki guda 200 da buhun shinkafa 1000 50kg da babura 200 da keken dunki da dama.
A wurin rabon wakilin Sanata Wamakko, shugaban matasan APC na jiha Alhaji Nasiru Itali ya ce wakkilcin Sanata ya wuce mazabar da yake wakilta, bayan an kare da kananan hukumomi takwas za a yi sauran kananan hukumomi 15.
 Mataimakin kakakin majalisar dokokin jiha Alhaji Kabiru Ibrahim Kware a lokacin taron ya jinjinawa Wamakko kan abin da ya gabatar.
Ya fahimci APC ta rufe dukkan jam'iyyun adawa a jiha hakan ya faru ne kan abin da take yi na taimakon talakawa.
A cewrsa Sanata Wamakko baya da shinge a taimakon jama'a da yake yi. 
"Tarihi baya iya tuna wani dan siyasa da ya taba ware buhun shinkafa 4000 ya raba, wanna kyauta ce babba."
Mai baiwa Gwamnan Sakkwato shawara kan hanyoyin karkara Honabul Malami Muhammad Galadanchi ya ce Sanata Wamakko ya yi abin da ya dace domin taimakon al'ummar da kake wakilta abu ne mai kyau.
"Sanata ya saba da taimakon jama'a koyaushe yana son haka don haka nan ban yi mamakin yanda ya fito da wadannan kayan aka rabawa jama'a musamman shinkafa da mutane za su ci su yi ibada ya samu lada.
"Wamakko zai cigaba da taimako ba tare da ya kula yanki shi ba, Sakkwato yake dubawa," a cewar Malami.