2023:Atiku Ya Lashe Zaben Fitar Da Gwani Na PDP
Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zaben fitar da gwani na jam’iyar PDP da aka gudanar a wannan Assabar.
Atiku ne dan takarar shugaban kasa a jami’iyar PDP in da ya samu mafi rinjayen kuri’un da aka jefa a wurin taron ya samu kuri'a 371.
Gwamnan jihar Rivers ne ya zo na biyu da yawan kuri’un da aka jefa in da ya samu kuri’a 237.
Sanata Bukola Saraki ne ya zo na biyu da yawan kuri’u 70.
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya samu kuri’u 20
Wakillai waton delegate 763 ne suka yi zaben a filin wasa na Abiola dake birnin Abuja, in da kuri'a 12 ta lalace, kuri'a 751 sahihan kuri'un da aka jefa.
managarciya