PDP  Ta Shirya Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi a Sakkwato-----Shugaban Jam'iya

PDP  Ta Shirya Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi a Sakkwato-----Shugaban Jam'iya

Shugaban jam'iyyar PDP a jihar Sakkwato Alhaji Bello Aliyu Goronyo ya tabbatarwa magoya bayan jam'iyar su a jiha cewa su; sun shirya shiga zaɓen ƙananan hukumomi a duk sanda aka shirya gudanar da zaɓen.
Shugaba Bello Goronyo ya sanar da hakan ne a wurin taron jam'iyar da ya gudana a birnin jiha ranar Lahadi, ya ce a matakin jam'iyarsu suna goyon bayan samar da 'yancin kai ga ƙananan hukumomi da gwamnatin tarayya ke son yi.
Goronyo ya ce suna sane da kuɗin da gwamnatin Sokoto ta karɓo a gwamnatin tarayya kuma za su yi bayani in lokaci ya zo.
Ya shawarci magoya bayan su da su yi haƙuri da ƙalubalen da ke cikin adawa hakan zai sa a cigaba da nasara a tafiya.