Dalilin Da Ya Sanya Ba Mu Rantsar Da Shugaban APC Na Sakkwato Ba------Gwamnan Neja

Dalilin Da Ya Sanya Ba Mu Rantsar Da Shugaban APC Na Sakkwato Ba------Gwamnan Neja

Muƙaddashin shugaban riƙon jam'iyar APC na ƙasa Abubakar Sani Bello ya karɓi rahoton kwamitin karɓa-karɓa na jam'iyya.
Rahoton da  shugaban kwamitin ya bayar Gwamnan Kwara Abdurrahman Abdulrazaƙ ya gabatar a hidikwatar jam'iyya dake Abuja, muƙaddashin shugaban ya yabawa kwamitin kan aikin da suka yi.

Da farko shugaban ya rantsar da shugabannin jam'iyar a jihohin Nijeriya ban da Sakkwato.
Ya ce kan maganar shugabancin APC a jihar Sakkwato za a samar da mafitar siyasa da za ta kawo shugaba a jihar da kowa zai gamsu da shi.

Gwamnan na nufin ba a rantsar da shugaban ne ba domin ba a samar da mafitar siyasa a jihar ba.