A Kowace Rumfa Mutum 10 Za'a Naɗa   S.A A Faɗin Sakkwato------Shugaban PDP

A Kowace Rumfa Mutum 10 Za'a Naɗa   S.A A Faɗin Sakkwato------Shugaban PDP

Alhaji Bello Aliyu Goronyo ya bayyana gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal matsayin wadda ta yi abin da yakamata a ɓangaren walwala da samar da romon dimukuraɗiyya a tsakanin 'yan siyasar jiha.

Shugaban PDP a wurin taron masu ruwa da tsaki da suke yi da ƙananan hukumomin jihar ne ya yi kalaman a wannan Laraba a gaban mutanen Illela ya ce gwamnatin ta samar da romon dimukaradiyya har cikin rumfunan zabe in da aka ɗauki mutum uku a kowace rumfa aka ba su bashi don samar da cigabansu.
Ya ce ko yanzu gwamna Tambuwal ya aminta da ba da S.A ga mutum 10, a kowace rumfa za a dauki matashi uku da mace uku da dattijai hudu kowane zai amfana da alawus na dubu 20  a kowane wata.
Yusuf Suleiman babban daraktan kamfe a Sakkwato  ya baiwa mutane hakuri kan abubuwan da suka faru a baya kan laifukan da aka yi musu.
Ya ce duk abin da mutum bai samu ba ya sani haka ne Allah ya ƙaddara don haka mutum ya dogara ga Allah.
Farfesa Aisha Madawaki mataimakiyar babban darakta ta ce  a wannan taron za su kara fahimta kan tafiyar da ake da ake yi.
Ta ce Tambuwal ya mutunta mata a jihar an dauki kansila 71 bayan sauran mukamai, amma mata na son kari kan abubuwan da aka yi masu