2023: Atiku Na Kokarin Rarrashin Wike, Wani Babban Jigon PDP Ya Koma APC a Kebbi

2023: Atiku Na Kokarin Rarrashin Wike, Wani Babban Jigon PDP Ya Koma APC a Kebbi

 

Wani jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a yankin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu, jihar Kebbi, Alhaji Jinaidu Wasagu, ya sauya sheka zuwa APC mai mulki. Hukumar Dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa tsofaffin shugabannin gundumomi da Sakatarori na cikin waɗanda suka sauya sheƙa tare da Wasagu a wani biki da aka shirya ranar Litinin a Kebbi.

Da yake maraba da masu sauya shekar, shugaban APC reshen jihar, Alhaji Abubukar Kana, ya taya su murnar shigowa jam'iyya mai farin jini, kamar yadda Punch ta ruwaito. 
Ya kuma ayyana sauya shekar babban ɗan siyasa kamar Wasagu a matsayin cigaba mai girma a jihar. Ya kuma tabbatar musu da cewa za'a tafi da su a dukkan harkokin siyasar APC a matsayin cikakkun mambobi. 
Da yake jawabi, Mista Wasagu ya yi ikirarin cewa sun ɗauki matakin tattara kayansu da barin PDP ne saboda zaluncin da ake musu da nuna musu wariya. 
"Ba hannu rabbana na taho ba, na tattaro shugabanni Takwas, Sakatarori da wasu dandazon zaɓaɓɓun shugabannin PDP a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu." 
"Iya mu'amalar Atiku Bagudu da ɗan takarar gwamna a inuwar APC, Alhaji Nasiru Idris, wanda ya nuna mana kauna duk da muna tsagin adawa, sune suka ja hankalin mu zuwa APC." Wasagu ya ƙara tabbatar da cewa akwai dumbin magoya bayansa da zasu biyo sawunsa sau da ƙafa zuwa APC ba wai a yankin Danko/Wasagu kaɗai ba har da yankin masarautar Zuru.