2023: APC Ta Nada Gwamnan Filato Matsayin Darakta Janar A Yakin Zaben Tinubu

2023: APC Ta Nada Gwamnan Filato Matsayin Darakta Janar A Yakin Zaben Tinubu

Jam’iyyar  APC ta sanar da nadin gwamnan jihar Filato, Simon Lalong a matsayin darakta-janar na yakin neman zaben shugaban kasa na Bola Tinubu. 

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan wata ganawa da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja. 
Adamu ya samu rakiyar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mataimakin dan takarar shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, da gwamnan jihar Filato, Lalong. 
Shugaban ya kuma bayyana nadin karamin ministan kwadago da samar da ayyuka Festus Keyamo a matsayin kakakin rikon kwarya kuma mawallafiyar jaridar LEADERSHIP Hannatu Musawa a matsayin mataimakiyar mai magana da yawun yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.