Fasto Ya Yi Hasashen Gwamna  Tambuwai Da Wasu Mutum 11 Dayansu Ne Zai Gaji Buhari

Fasto Ya Yi Hasashen Gwamna  Tambuwai Da Wasu Mutum 11 Dayansu Ne Zai Gaji Buhari

 

A yayin da zaben 2023 ke kusatowa an fara neman wanda zai dare kujerar shugaban kasa bayan shugaba Buhari ya kammala wa'adinsa.

Babban Fasto Primate Ayodele ya yi hasashen wadan da yake ganin za su iya zama shugaban kasa anan gaba in da ya zayyano Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum da Tsohon shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki da Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Ministan Shari'a na kasa Abubakar Malami da sauransu cewa daya daga cikinsu ne zai gaji Buhari.

Faston ya nuna Manyan 'yan takarar shugaban kasar waton tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da jagoran APC Bola Tinubu ta su ta kare a zama shugaban kasa.
A cikin haka ne babban faston cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya saki hasashensa na abubuwan da za su faru a 2022.
Amma kuma, Primate Ayodele ya ambaci sunayen wasu gwamnoni da manyan kasar cikin wadanda ka iya darewa kujera ta daya a kasar. 

Daga cikin wadanda ya ambata a bangaren jam'iyyar  PDP akwai; Aminu Waziri Tambuwal, Nyesome Wike, Bukola Saraki, Samuel Ortom da Bala Mohammed Ya kuma ambaci Rabiu Musa Kwankwaso da Emmanuel Edom a matsayin wadanda ka iya yin nasara. 
Har wa yau, Ayodele ya ambaci Abubakar Malami, Boss Mustapha, Kayode Fayemi, Rotimi Amaechi, Prof. Babagana Umara Zulum, Babatunde Fashola, Mai Mala Buni, Ibikunle Amusun, da Aregbesola Rauf a bangaren APC. 
Abin jira a gani a hasashensa tashin farko sai an tsayar da 'yan takara tukun kafin a iya fara yadda da hasashen ko jefar da shi.

Hasashe ne kawai aka yi ba tabbas cikin zancensa tun da rayuwa da abin da zai same ta ikon Allah ne da saninsa shi kadai.