Dan takarar Gwamnan jihar Zamfara a jam'iyar PDP Alhaji Dauda Lawal Dare ya bayyana cewa yana neman zama Gwamna ne domin magance matsalar tsaron Zamfara da ake ta fama da shi, tsawon lokaci wanda zaluncin shugabanni ne ya sa lamarin yake a haka.
Lawal Dare a wurin yekuwar zabe da ya gudanar a karamar hukumar Kauran Namoda ya sanar da cewa harkar ilmi ya tabarbare a jihar.
"In muka samu dama za mu biya kudin jarabawar Sikandare da wannan gwamnati kasa biya, dalibban da aka tura a waje Sudan da sauran wurare suna fama da wahala a in da suke gwamnati ta kasa biya masu kudin karatu, suna kwana a waje wanda ba za mu yarda da hakan ba."
Dauda ya yi kira ga magoya bayansa su karbi katin zabe don da shi ne kadai za su iya zabarsa har a samu nasara.
Sannan ya yi kira ga matasa da suke tafiya wurin kamfensa "kar a yi amfani da ku a je a sari wani ko jima wani a Zamfara." a cewar Dauda.