Canja sheƙa: Mun Karɓi Kurame Da 'Yan Gudun Hijira a PDP----Uwani Hamsal

Canja sheƙa: Mun Karɓi Kurame Da 'Yan Gudun Hijira a PDP----Uwani Hamsal

Daga Habu Rabeel, Gombe

A lokacin da zaben shekarar 2023 ke ta kara karatowa da ake daf da kaddamar da fara yakin neman zabe Shugabar kungiyar Reporters awareness ta jam'iyyar PDP a jihar Gombe Hajiya Uwani Hamsal, tace sun karbi yan gudun Hijira da kurame da suka haura sama da dubu uku a jam'iyyar PDP.

Hajiya Uwani Hamsal, ta bayyana hakan ne a taron mana Labarai da ta kira inda tace canja shekar na yan gudun Hijira dubu biyu da kurame dubu daya da dari biyar ya nuna cewa dan takarar gwamnan Gombe na jam'iyyar PDP a Gombe Muhammad Jibrin Dan Barde, zai kai ga samun nasara a zaben dake tafe na 2023

Hajiya Uwani Hamsal, ita ce ta jagoranci karbar wadanda suka canja shekar daga APC zuwa PDP a madadin dan takarar Muhammad Jibrin Dan Barde, inda suka ce rashin adalci ne yasa suka canja sheka.

A cewar ta tana da tabbacin Muhammad Jibrin Dan Barde, ba zai basu kunya ba  domin mutum ne mai fada da cikawa da kuma kaunar juna domin shi ya shiga siyasa ne ba dan handama da babakere ba sai dan ya samu yadda zai ciyar da al'umma da kuma  jihar sa gaba.

Ta kara da cewa jam'iyyar PDP jam'iyya ce mai adalci wacce ba ta da banbanci kowa nata ne dan haka shigowar su jam'iyyar a wannan lokaci sara ne akan gaba domin suna da rawar takawa a lokacin zabe.

Daga nan Uwani Hamsal, ta ja hankalin su da cewa su tabbata kowa yana da katin zaben sa dan shi ne makamin da za su yaki tsohuwar jam'iyyar da suka fice dafa cikin ta ta APC.

A jawaban su mabanbanta da suke bayyana dalilan su na ficewa daga tsohuwar jam'iyyar su ta APC yan gudun hijirar da Kuramen cewa suka yi rashin adalci ne da kuma yadda aka gaza taimaka musu.

Inda suka ce dasu aka kafa gwamnati amma tunda aka ci zabe aka watsar da su yan gudun Hijira kuma ake ci da bazar su kuma ana cewa ba yan gudun hijira duk da ana tawo tallafi dan a basu amma ba'a basu.