Zaɓen 2023: Matasan Arewacin Yobe Suna Goyon Bayan Hon. Bashir Machina
Daga Muhammad Maitela, Yobe
Gamayyar kungiyar matasan Arewacin Yobe, 'Yobe North Youths Alliance' ta bayyana cikakken goyon bayan ta ga Dan takarar majalisar dattawan Nijeriya, wanda ya kunshi kananan hukumomin Bade, Jakusko, Yusufari, Karasuwa, Nguru da Machina, Hon. Bashir Machina. Tare da bayyana cewa sun dauki matakin bayan tuntubar ilahirin matasan yankin tare da cancantar sa da gogewa a siyasa da mu'amala.
A zantawar wakilinmu da Kwamared Muhammad Nura Gashuwa, bayan rangandin da kungiyar ta gudanar a yankin, tare da tuntubar kowane bangare. Ya ce matasan sun cimma wannan matsayar ne baya ga la'akari da suka yi da nagartar Hon. Machina wanda suka ce ko shakka babu zai yi wa yankin wakilci nagari a zauren majalisar dattawan Nijeriya, idan ya samu amincewar al'ummar Arewacin Yobe.
"Wannan yanki na Arewacin Yobe ya na bukatar mutum irin Hon. Bashir Machina saboda gogewar sa a harkokin siyasa tare da mu'amala da jama'a. Sannan kuma mutum ne mai sauraren ra'ayoyin jama'a, kyakkyawar fahimta da girmama kowa da kowa. An san shi da kwatamta gaskiya da rikon amana. Kuma mutum ne mai kwazo kuma karbabbe a gun kowa." In ji shi.
"Al'ummar wannan yankin shaida ne dangane da ayyukan ci gaba da ya samar wa wannan jihar baki daya, tsawon lokacin da ya zauna a hukumar kula da Jiragen Ruwa ta Nijeriya, kana kuma ya samar wa matasa ayyukan yi, tallafin karatu da makamantan su. Wanda muke ganin idan jama'a suka bashi dama zai kawo ci gaba mai ma'ana a Arewacin Yobe."
Muhammad Nura ya kara da cewa, "Idan an kalli gwagwarmaya da fadi-tashi a fannin siyasa, Hon. Bashir Machina kwararre ne kuma ya yi an gani, saboda yadda ya kawo ci gaba mai dimbin yawa ba a yankin sa kadai ba, ilahirin jihar Yobe an ci gajiyar sa."
"Saboda haka muna kira ga baki dayan al'ummar kananan hukumomin Arewacin Yobe shida (6) su bai wa Hon. Bashir Machina goyon baya, su zabe shi a matsayin dan majalisar dattawa, domin samun ci gaba mai ma'ana." Ta bakin Alh. Nura.
managarciya