Gwamnonin Arewa Maso Gabas  Sun Ba Da Gudunmuwar Miliyan 20 Ga Mutanen Goronyo

Gwamnonin Arewa Maso Gabas  Sun Ba Da Gudunmuwar Miliyan 20 Ga Mutanen Goronyo
Gwamna Zulum
Gwamnonin Arewa Maso Gabas  Sun Ba Da Gudunmuwar Miliyan 20 Ga Mutanen Goronyo
Sati ɗaya bayan kai hari a Kasuwar Goronyo aka kashe mutane da yawa, gwamnoni shidda daga yankin Arewa maso Gabas sun baiwa mutanen da harin ya rutsa da su tallafin miliyan 20 ta hannun gwamnatin jihar Sakkwato.
Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ne ya sanar da gudunmuwar gwamnonin yana tare da rakiyar Gwamnan Gombe Yahaya Inuwa a lokacin da suka kawo jaje ga gwamnatin Sakkwato da kuma waɗanda lamarin ya rutsa da su a ranar Assabar.
Gwamna Zulum wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnoni a yankin ya nuna ɓacin ransa ga abin da ya faru da kuma hada kai domin a yi maganin abin da ke faruwa na mahara da ɓarayin shanu.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yaba masu kan wannan hoɓɓasar da ba su tabbacin gwamnatinsa ba za ta yi wasa ga darasi da ta dauka kan maƙwabtan jihohi ba.
Tambuwal ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta ƙara samar da kayan aiki ga jami'an tsaro domin yaƙar mahara da ɓarayin shanu.