'Yan Nijeriya Sun Kama Kifi Mafi Sauri A Duniya Kudinsa Ya Haura Naira Dubu 600
Daga Comrd Yusha'u Garba Shanga.
Wasu matasa 'yan Najeriya sun kama wani kifin ruwa mai suna Sailfish a lokacin da suke bakin aiki wurin ruwa a jihar Legas.
Daya daga cikinsu wanda Injiniyan Ruwa ne ya sanar da kame dabbar da ake kira amphibian wacce ita ce kifi mafi sauri a duniya.
Da yake magana a shafinsa na Tuwita, @Mista_YPNation ya raba hotunansu rike da kifin akan wata na’ura kamar yadda ya bayyana cewa suna amfani da shi wajen shirya barkonon tsohuwa.
A cewar yankin Facts na Afirka, cikakken girman Sailfish ya kai kimanin $1,500 a kasuwar duniya (kimanin N623,000).
managarciya