Matar Shugaban DSS Ta Zagi Iyayena Tare Da Alwashin Ba Zan Yi Gwamna Ba---Gwamnan Kano

Matar Shugaban DSS Ta Zagi Iyayena Tare Da Alwashin Ba Zan Yi Gwamna Ba---Gwamnan Kano

 

Abba Kabir Yusuf ya fito ya fayyace abin da ya wakana tsakaninsa da matar shugaban hukumar DSS, Aisha Yusuf Bichi a farkon shekarar nan. 

Legit.ng Hausa ta fahimci Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi zama da malaman jihar a gidan gwamnati domin yin godiya kan kawo zaman lafiya. 
Mai girma Gwamnan ya yi amfani da damar wajen bada labarin bangarensa na sabanin da ya samu da mai dakin Yusuf Magaji Bichi a filin jirgi. 
A bidiyon da aka wallafa a shafin tashar Rahma, an ji Abba Kabir Yusuf yana cewa Hajiya Aisha Bichi ce ta auka masa da zagi babu gaira babu dalili. 
Abba Gida Gida ya zargi matar shugaban hukumar tsaron da zagin iyayensa har da yi masa barazanar cewa ba zai yi mulki ba, a yau shi ne Gwamna. 
A cewar Abba, tun farko ya je wajen matar ne domin ya fada mata abin da yaranta ke yi, mikewarta ke da wuya, ya ce sai ta zarge shi da rashin kunya. 
Ko da ya samu sabani da Aisha Bichi, Gwamna Abba ya nuna akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da mai gidanta wanda shi ne ke rike da DSS. 
Ganin ya san mai gidanta, sai ‘dan takaran na NNPP (a lokacin) ya nemi tuntubar shi domin sanar da shi abin da ya faru, amma bai same shi a salula ba.