Gwamnan Zamfara Ya Rabawa Jami'an Tsaron Sakai Motoci Da Mashuna 1,500
Daga Comr Abba Sani Pantami.
A jiya litinin maigirma gwamnan jihar Zamfara Dr. Bello Matawalle ya yi ganawar sirri da jami'an tsaro da sarakuna 19 da kantomomin kananan hukumomi 14 a farfajiyar gidan Gwamnatin jihar Zamfara.
Bayan kammala tattaunawar na tsawon lokaci Gwamnan ya rabawa jami'an tsaron sakai civilian JTF motoci kirar Helux 20 da mashuna 1,500 domin kare kai a kokarin shi na kawo karshen matsalar rashin tsaron da ya addabi jihar da ma Arewacin Najeriya baki daya.
Gwamna Matawalle tare da jami'an tsaro, sarakuna da kantomomin kananan hukumomi sun sake saka sabbin dokoki a jihar domin ganin aikin jami'an tsaro ya tafi yadda ake so.
Ga sabbin dokokin kamar haka;
1, An hana hawa mashin daga karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe a unguwanni kamar haka; Gada Biyu, Janyau ta Gabas, Sinami, Mareri da Damba Barakallahu dake cikin garin Gusau.
2, An hana ko wane hotel bada matsugunni, face mutum ya gabatar da katin dan kasa ko katin zabe ko katin kasa da kasa ko lasisin tukin mota.
3, An hana duk wani taron siyasa, sai lokacin da hukumar zabe ta kasa INEC ta ayyana.
An kuma bada lambobin kiran gaggawa na musamman 112 domin bada bayanan sirri akan matsalar tsaro, da kuma kira domin ko ta baci, kuma kiran lambar kyauta ce.
managarciya