Tsohon shugaban karamar hukumar Tureta a jihar Sakkwato Alhaji Munde Loha ya rasa iyalansa shidda mata da direban mota daya abin da yakai yawansu su bakwai a wani hatsarin mota da ya faru da su saman hanyarsu ta zuwa Argungu daga Sakkwato.
Wata majiyar ta ce matan sun bar gida ne za su tafi buki dukkansu dangi daya ne mata da 'ya'yan tsohon shugaban karamar hukumar ne suka hadu da ajalinsu a lokaci daya kafin su isa garin Argungu.
An yi wa margayan sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanadar, a lokacin da dangi da masoya ke cikin alhinin rashin iyalan gaba daya.