Mukhtari Shagari Ya Fita Daga Jam'iyar PDP 

Mukhtari Shagari Ya Fita Daga Jam'iyar PDP 

 

Tsohon mataimakin Gwamnan Sakkwato Barista Mukhtari Shehu Shagari ya fita daga jam'iyar PDP wadda ya dade cikinta tun kafuwar jam'iyar bai fita ba.

Sauya shekar ya biyo bayan matsayar da gwamnan Sakkwato Aminu Waziri ya cimma na tsayar da tsohon sakataren gwamnatinsa Alhaji Sa'idu Umar Malam Ubandoma domin ya gaje shi a 2023.
Barista ya sanar da wannan matsayar ne a turakarsa ta facebook in da ya ce nabar jam'iyar PDP daga yau(Laraba) zan kuma sanar da matakin da zan dauka na gaba.
Duk kokarin jin tabakin Barista Mukhtari Shagari abin ya ci tura, domin bai daga wayar da aka kira ba.