'Yan Daba Sun Farmaki Wurin Ibada Ana Cikin Zanga Zanga a Katsina

'Yan Daba Sun Farmaki Wurin Ibada Ana Cikin Zanga Zanga a Katsina

 

Wasu ƴan daba sun kai farmaki wata coci mai suna Living Faith da ke ƙaramar hukumar Daura a jihar Katsina. 

Ƴan daban a yayin farmakin sun sace kujeru kusan 205, da kayan kaɗe-kaɗe, da wasu kayayyaki na miliyoyin naira. 

Ƴan daban sun dira a cocin ne yayin da ake zanga-zangar #Endbadgovernance a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar Leadership. 
Faston da ke kula da cocin, David Jatau, ya bayyana cewa sun kasa gudanar da ibada a ranar Lahadi saboda ƴan daban sun kwashe dukkanin wani abu da ke cikin cocin a lokacin zanga-zangar, rahoton The Nation ya tabbatar. 
"Muna da jami'an tsaro biyu da ke aiki a cocin, ɗaya yana bakin aiki yayin da ɗayan ya tafi hutu. 
Lokacin da aka fara zanga-zangar da misalin ƙarfe 10:00 na safe, ƴan daban kawai sai suka taho cocin." 
"Da yawa daga cikinsu suna cikin Keke Napep, sannan suka fasa ƙofofi da gilasai suka shige cikin cocin." 
"Sun kwashe komai da ke cikin cocin da suka haɗa da agogon bango, kayan kiɗa, kujerar fasto, kujerun roba da kwamfuta. Sun lalata komai." 
Ya ƙara da cewa cocuka uku aka yi hari amma ƴan daban sun yi nasara ne kawai a cocin Living Faith Church da Deeper Life Church, amma sun kasa shiga cocin Anglican Church saboda ƙofar cocin na da ƙarfi sosai. 
Ya bayyana cewa sun gayawa ƴan sanda da sojoji abin da ya faru, inda a jiya suka sanar da su cewa sun kama wasu mutane.