SHARAƊIN EFCC KAN SAKI TAMBUWAL

SHARAƊIN EFCC KAN SAKI TAMBUWAL

 An sako tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal daga hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), kamar yadda Daily Trust ta tabbatar. 

Tambuwal, wanda aka tsare tun jiya ranar Litinin a hedikwatar hukumar na hukumar, ana zarginsa da almundahanar naira biliyan 189 a lokacin da yake rike da mukamin gwamnan jihar sa. 

Tsohon gwamnan ya amsa gayyatar da aka yi masa ne da misalin karfe 11:16 na safiyar ranar Litinin, kafin daga bisani a tsare shi bayan da aka ce ya kasa bayar da amsar tambayoyin da aka yi masa. 

Da yake tabbatar da sakin sa ga wakilinmu, daya daga cikin jami’an hukumar ya ce an ba da belin shi, kuma da zarar ya cika sharudda za a sallame shi.

Da aka tambaye shi ko za a tuhume shi da kuma yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu, bai ce komai ba. 

Wakilinmu ya kira mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale, domin jin ta bakinsa game da lamarin amma hakan bai yiwu ba, kuma har yanzu bai amsa sakon da aka aike masa ba.