Matawalle Zai Yi Abin Da Zamfarawa Za Su Ji Dadi Bayan Faduwa a Kotun Koli

Matawalle Zai Yi Abin Da Zamfarawa Za Su Ji Dadi Bayan Faduwa a Kotun Koli



Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya amince ya yi aiki tare da Gwamna Dauda Lawal na Zamfara. 

Matawalle ya ce sun karbi hukuncin Kotun Koli hannu bibbiyu kuma suna yi wa Gwamna Dare fatan alkairi. 
Ministan ya bayyana haka ne yayin hira da DCL Hausa inda ya ce zai ba da dukkan gudunmawa don ci gaban jihar Zamfara. 
"Ina kira ga Gwamna Dauda Lawal ya rike duk dan jihar Zamfara ba tare da bambanci ba. 
"Yanzu siyasa ta wuce ya kamata mu hada kai don samar da tsaro a jihar Zamfara kuma ina fata a wannan lokaci na shi a kawo karshen matsalar tsaro. 
"A matsayin na Minista a ma'aikatar tsaro zan ba da dukkan gudunmawa don tabbatar da tsaro a Zamfara da Arewacin Najeriya da ma Nijeriya baki daya." 
Matawalle ya bukaci gwamnan da ya dauki kowa dan uwansa a sha'anin Zamfara inda ya shawarce shi da ya guji wasu shawarwari da ba su dace ba. 
Wannan na zuwa ne bayan Bello Matawalle wanda ya yi takara a jam'iyyar APC ya gaza yin nasara a Kotun Koli.