ANA BARIN HALAL...: Fita Ta 21
ANA BARIN HALAL..
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*PAGE* 21
*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559
***********
Bayan goggo ta tsaya sun gaisa da Aunty rashida sai tayiwa goggo tayin ta shigo su rage mata hanya, babu yadda goggo ta iya dole ta shiga suka rage mata hanya har zuwa ƙofan gidan mu, domin Aunty Rashida da gewa tayi dole sai da goggo ta shiga, suna sauƙe ta suka wuce, shigowan goggo ta gayawa innah yadda duk sukayi a asibiti, da yadda zata dinga zuwa duk bayan sati biyu, wannan ba baƙonta bane tunda haihuwa bana fari bane.
Babu wuya wurin ubangiji yau Goggo ta tashi da naƙuda tun wurin asuba, amma bata gayawa kowa ba sai yayah auwalau da ya fahimci bata jin daɗi, zuwa yayi kusa da ita yana mata sannu, ɗaga kai kawai tayi alaman ta amsa mishi, shi ko ganin haka ya nemi gefen gadonta ya zauna, dayake tunda ta shiga wata na takwas sai inna ƴan biyu ta karɓi hidiman masan, amma duk da haka yaya auwal ne ke haɗa mata ƙullin masa, wani lokacin ma sai yafara soyawa take fitowa, saboda daga Yayah Auwal, yayah sani, yayah rabi'u duk sun iya haɗawa, amma rabi'u baya soyawa, yawanci ma shara da wanke-wanke shi da yayah sani sukeyi, juyawa goggo tayi tana kallon yayah auwal, "Kaje ku gyara gidan suyi shirin makaranta, kai kuma ka fara haɗa ƙullin masan kafin inna ta fito, amma ka fara kai mun ruwan wanka ko ɗan albarka", ta ƙarasa tana dafa kanshi fuskan ta ɗauke da murmushi, shima murmushin yayi ya tashi yaje yin abubuwan da ta lissafa mishi, suma yayuna duk sun shigo sun gaishe ta sannan kowa ya fara aikin shi na kullum, yayah sani ya kaiwa su hassan da hussain ruwan wanka suka fara kafin goggo ta miƙe da ƙyar taje tayi wankan, fitowan tane suka haɗu da inna taga alaman goggo naƙuda takeyi, da hanzari ta nufeta tana mata sannu, "Fatima abun ne yazo"? Goggo ta ɗaga kai alaman shine, ajiye butan hannun ta innah tayi ta riƙota suka ƙarasa ɗaki, abinda zai baki mamaki innah dama tana son goggo, da Baba garba kuma ya rasu sai innah ta sake jin tausayi da ƙaunar ta, dole ta maida goggo kamar ƴar cikinta ba surkuwa ba, domin ganin goggo marainiya ce babu uwa babu uba, babu wa babu ƙani, dama hannun kakarta ta wurin uwa ta girma,
Babu ɓata lokaci suka shiryah innah ƴanbiyu ta rakota suka shiga napep ɗin da yayah auwal ya taro musu, hannun innah riƙe da kayan babyn da duk yawancin su Aunty Rashida ne ta tsinta mata a sayayyan da sukayi, wasu kuma a ribar masan take tsinta a gwanjo, duk jikin yayuna yayi sanyi suka tsaya suna kallon napep ɗin har ya bar gidan, da ƙyar suka shigo gida suka yi shirin tafiya makaranta, yayah auwalu kuma ranan bazai samu zuwa ba, saboda shi zai kula da komai na gidan, Alhamdulillahi goggo bata barin ƴaƴanta nan haka kara zube, don ganin babu mace bata barsu sun zauna babu aiki ba, kowa yana aiki a cikin su.
Goggo nah bata samu kanta ba sai wuraren bayan sallan la'asaar, wuraren ƙarfe biyar na yamma, goggo na tasha wahalan naƙuda na yadda tace, ta wahala sosai a haihuwana, sai wannan lokacin Allah ya nufa zan iso duniya, shiyasa na kasan ce mai sanyin hali da haƙuri, kodan saboda lokacin zuwana duniya tayi sanyi? Ga gidan na a sanyaye cike da wahala da mawuyi na rayuwa"? Ya faɗa yana ɗago kanshi fuskan shi ɗauke da murmushi yana duba na, sauƙe kaina nayi ƙasa saboda wani irin tausayin shi da naji ya rufe ni alokacin dana kalli fuskan shi naga yanayin da yayi maganan, murmushi yayi ya cigaba da bani labarin.
*********
Lokacin da suka dawo daga asibiti duk suka taru a jikin babyn, yadda ake bani labari kusan raino na a hannun yayah auwalu ne, kafin su dawo dama ya gyara ɗakin goggo tsaf, ya haɗa kayan ta na wanko duk ya wanke, sannan ya yi abinci dafa dukada wake na manja, bayan an ɗan lafa da shigowa kallon jaririn , an mishi wanka tsaff an saka shi akayan sanyi masu kyau goggo ma tayi wankanta tsaf, yayah auwal ya kawowa goggo abincin har ɗaki taci, daga innah har inna ƴanbiyu sai albarka suke sakawa yayah auwalu.
Bayan sallan magarib inna ta aiki ƙanin mijinta bappan su Baba Garba wurin mahaifina akan ya faɗi haihuwa na, haka kuwa akayi ana sallan magrib yaje massalacin ƙofar gidan mu sukayi magana da baba na, bai shigo ba sai bayan yayi sallan ishaa ya shigo gidan mu wurin innah, kinsan me Babah na ya aiko? shiru yayi kaman bazai sake cewa komai ba, har na ɗago kai na kalle shi, sai naga ya ƙurawa wuri guda ido, chan kuma sai ya dawo da kallon shi kaina, murmushi yayi mai kyau ya cigaba da bani labarin.
"Cewa yayi a gayawa goggo da ita da ɗanta duk baida buƙatansu har abada, da aka mishi magana sunan da za'a saka sai ya sake cewa duk sunan da ya mata ta saka shi dai baida buƙatan ta dangana shi da yaron har abada ya bar mata, kowa sai da jikin shi yayi sanyi a lokacin, kuka innah ta fara tana ambata wannan masifah da mai yayi kama, shi kuma irin na shi jarabawan kenan ɗan jaririn da bai san komai ba? Murmushi goggo tayi bata tufah komai ba sai ido da ta zubawa jaririnta, hannu yayah auwa ya saka ya ɗauke ni daga cinyar goggo, a hankali ya kai bakin shi kunne na ya mun huɗuba da sunan *MUKHTAR* miƙani hannun innah yayi yace, "Inna ga *MUKHTAR GARBA* ki saka mishi albarka" ido kowa ya ƙura mishi, Bappan su Baba ne yayi ƙarfin halin cewa, "sunan wa kasaka mishi malam muhammadu auwal"? Hawaye innah ta goge a fuskanta tace "sunan wa kuwa zai saka bayan na mahaifina, sunan mahaifina ya saka mun, wanda Mahaifin shi yaci burin sakawa Allah bai nufa ba har ya bar duniyan", tana faɗa ta rungume yayah auwalu tana kuka tana saka mishi addu'a, tana kuma adduan Allah ya bashi ikon riƙe ƙannen shi,
Ranan suna naci sunan mahaifin innah wato *MUKHTAR* wanda ko ragon suna ba a yanka mun ba, saboda innah da goggo basu da shi, dabino ma, haɗa kuɗi innah da goggo sukayi, domin innah tana sayar da kananzir, Aunty rashida ta shigo barka washe garin haihuwa na, lokacin tayi ta santin kyauna da fari na, ta ringa addu'an Allah ya bata ɗa fari itama, domin mahaifin A.G fari ne, itace baƙa, ranan suna kuwa da Azahar Allah ya sauƙe ta lafiya ta haifi A.G, shiyasa A.G akwai zafi don da rana tsaka aka haife shi, M.G ya faɗa yana dariya, idon shi ya mayar yana kallon A.G, nima dariyan naji yazo mun lokacin da na dubi idon A.G naga ya wani haɗeta kaman zai fashe don fushi, dariyan da mukeyi ne ya wani juyo yana hararan M.G, ni dariyan da na ƙara ji ganin yana wani jijjiga kai kaman shi ne babba, muna lafawa M.G ya kalleni yace,
"Haihuwar A.G yazo mana da alkhairi ba kaɗan ba, domin ranan sunan A.G kakanshi raguna biyu ya saya, Baban shi ya sayo ɗaya, ganin haka Aunty Rashida ta aiko ɗaya wa goggo akan a yanka wa mun, ranan su Yayah Rabiu kaman zasuyi yayah.
Haka akaita rainon mu har mukayi shekara uku, kuma tun bamu wuce watanni ba Aunty Rashida ta fara zuwa kitso gidan mu, daga madaran da A.G yake sha har friso ɗin shi Aunty Rashida bani takeyi, daga baya ma yaƙi sai kunun su alkama, haka take sakawa a haɗa har dani, sannan ta saya mana kaya tare, bamu wuce 2years ba muka shaƙu da shi, idan sunzo zasu tafi na ringa ihu kenan, muna cika 3yrs kuwa Daddyn shi ya saka mu school tare, lokacin Daddy ya tafi karatu waje, Aunty Rashida ta dawo gidan kakanun shi da zama, kafin muyi 5yrs Daddy ya dawo mun yi wani irin shaƙuwa na fitan hankali, don ma Allah ya saka mun ɗafa na uwa ne, kuma Yaya auwal ya kasa ya tsare akan kula da tarbiyana, yaƙi barin na ringa kwana a gidan su A.G, kullum cewan shi rayuwar su da cimansu ba irin namu bane, idan na buɗi ido da nasu zan raina ƙoƙarin su, kuma jin ƙan su zai mun sauƙi, sai dai naje nayi wasa na dawo gida, gashi an koya mun rashin cin abinci a gidan mutane, sai yazama duk sabon mu akwai ƙarancin cin abincina a gidan su, sai dai shi A.G wataran yakan biyo ni da abincin gidan mu muci,
Tun tashin mu A.G bai cika sakewa da mutane ba, sannan maganan shi a taƙaice suke, kuma is hardly kiga murmushin shi ko yawan dariyan shi, amma A.G yana da kirki da kyawawan halaye da har yau ban taɓa ganin irin shi ba, idan kinga dariyan shi ko murmushin shi ko maganan shi tou muna tare da shi ne, shima sai idan mu biyo ne babu wani, don shi ko da Aunty Rashida, wato mummyn shi baya wani dogon hira da ita," "yana dai da baƙin hali"na faɗa ina kallo inda A.G ɗin yake zaune, kaman yasan maganan shi nayi kuwa ya ɗago idon shi ya sauƙe akanmu, murguɗa baki nayi na ɗan harare shi, jijjiga kai yayi alaman zamu haɗu, dariya M.G yayi daga dukkan alamu ya kalli abunda ya faru, "kawai dai kin kasa fahimtan shine amma A.G mutum ne har da ƙari, gashi shi kuma ya fahimce ke mai kirkice da mutunci",
Kallon shi nayi ina zare ido alaman tambaya, lumshe kyawawan idon shi yayi ya sake buɗesu akaina, murmushin shi nagado ɗauke a fuskan shi yace, "A.G yana yaba hankalinki da nutsuwar ki, amma yanzu naga baki da aiki sai hararan ɗan uwa na, kuma zan ɗauki mataki mai tsauri akan haka" ya faɗa yana dariya, nima dariyan nayi na rufe fuskana nace, "shi bakaga harara na shima yakeyi ba?"
"Nashi na tsawatar wane, naki kuma kin fara raina mun hussaini na ne"
Murmushi nayi nace "tou na daina, amma shima kace ya daina"
"angama ranki ya daɗe" ya faɗa yana wani risinawa na neman tsokana, wanda dukkan mu saida mukayi dariyan hakan.
************
Wannan shekaran yayah auwal ya tafi university a chan LAGOS. Wannan tafiyan sai yazama kaman gidan mun ɗan shiga wani yanayi na takura, domin haxaƙan yayah auwal ba iri ɗaya bane dana yayah sanie, shi baida juriya da hidima, barshi dai da taya goggo irin su shara wanki, har da namu shi yake yi, amma har kan neman abun amfani baida wannan kuzarin, shi kuma Yayah rabiu zaman shi gida ba sosai ba kullum yana filin ƙwallo, duk yadda akayi da shi haka aka barshi, ƴan biyu ne ma suke ɗaukan tallen kananzir ɗin inna suna fita mata, ni kuma banyi wani wayon kirki ba, duk da hakama ina da ƙoƙarin karɓo kwanon masu sayan masa a waje na kawo, idan an zuba na miƙa musu, domin ni ina da ƙoƙarin kaman ba mai shekara biyar ba, don Allah yayi ni da halittan ƙarfi da tsayi, don duk wanda ya kalle ni yaga *ALƘALI ABDULLAHI* don daga kamannin har zubin halittana nashine, farin fatan goggo kawai na ɗauka, duk ƴaƴan Alƙali ba mai kama da shi iri na,
Zakice muna unguwa ɗaya yayah haɗuwan mu da mahaifina yake ko ƴan'uwa na ko?
*AUNTY NICE*
managarciya