Ɗalibban Kebbi 24 sun shaƙi iskan 'yanci
Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa an sako ɗalibai mata 25 na makarantar GGCSS, Maga a Jihar Kebbi, da aka yi garkuwa da su a ranar 17 ga Nuwamba.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar cewa an sako su ne da safiyar Talata, ta hanyar haɗin gwiwar Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA) da Hukumar Tsaro ta DSS.
Majiyar ba ta bayar da ƙarin bayani ba, amma ta raba hotunan ɗaliban da aka kuɓutar.
managarciya