Gwamnatin Buhari Ta Ce Ba Za Ta Ciwo Bashi Don Kawo Karshen Yajin Aikin Malaman Jami'a 

Gwamnatin Buhari Ta Ce Ba Za Ta Ciwo Bashi Don Kawo Karshen Yajin Aikin Malaman Jami'a 

Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo, ya bayyana a jiya cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da hurumin ciyo bashin Naira Tiriliyan 1.2 a duk shekara domin warware yajin aikin da kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) su ka shiga. 

Rahoton THE NATION Martanin Festus Keyamo kenan a lokacin da yake amsa tambayoyi a gidan talabijin na Channels 
Keyamu yace matsin lamba kungiyar ASUU ba zata sa gwamnati ta ciyo bashin Naira Tiriliyan 1.2 dan biyan bukatun ta ba, wanda idan aka yi la’akari adadin kudin shiga da kasar ke samu, bai wuce Naira Tiriliyan 6.1 a lokacin da muke da hanyoyin, cibiyoyin kiwon lafiya da za mu gina, ga kuma sauran fannoni da ke bukatar kulawa a kasar. 
Daga nan Festus Keyamu ya bukaci iyaye a fadin kasar da su rika rokon kungiyar ASUU ta janye yajin aikin da take yi.
Keyamu yace, yakamata su koma bakin aikin su, saboda basu kadai bane hukumar dake ci daga asusun Najeriya ba, Najeriya baza ta tsaya cak saboda an kasa biyan bukatun ASUU ba.