Jaririya 'Yar Wata 3 Da 'Yan Bindiga Suka Sace A Zamfara An Yi Masarar Ceto Ta

Jaririya 'Yar Wata 3 Da 'Yan Bindiga Suka Sace A Zamfara An Yi Masarar Ceto Ta

Jaririya 'Yar Wata 3 Da 'Yan Bindiga Suka Sace A Zamfara An Yi Masarar Ceto Ta

Rundunar 'yan Sanda na jihar Zamfara sun samu nasarar ceto wata jaririya mai wata uku da 'yan bindiga suka tafi da ita.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ayuba Elkanah, ne ya bayyana haka, a wani taron manema labarai a Gusau, a ranar Laraba.
Ya ce an sace jaririyar ce a kauyen Ruggar Tudu da ke Karamar Hukumar Bungudu ta jihar.
Ya ce 'yan sanda sun samu nasarar cafke wasu maharan dauke da bindigogi da makamai kan wannan ta'addanci.
A cikin abubuwan da aka gani  a wajensu har a baburan hawa, bindigogi kirar AK-47 guda takwas, makamin harba roka guda daya da kuma harsasai masu yawa.