Na yi Nadamar Yin sulhu da 'yan Bindiga----Masari
Na yi Nadamar Yin sulhu da 'yan Bindiga----Masari
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana cewar, sam babu wani cigaba ko nasara da ake samu a harkar tsaro sakamakon tsayawa yin sulhu da yan ta'adda.
Gwamna Masari ya ce, ba sau daya ba yayi zaman tattaunawa da yan tada kayar baya amma babu wani canji da aka samu a jihar Katsina.
Gwamnan na Arewa ya bayyana rashin amuncewar sa na yanzu tsayawa sasanci da yan bindiga ya nemi gwamnatoci kawai su runta ma musu da ruwan wuta da alburusai.
Aminu Bello Masari ya nuna damuwa da takaici kan halin rashin tsaro a jihar sa inda yace zai dau mummunan mataki kansu kuma ba zai sake neman afuwar su ba.
Tuni da gwamnan ya haramta sana'ar canjin wayoyi da batura na salula domin toshe wata kafa kan dakile matsalar rashin tsaro a jihar.
Haka ma ƙananan hukumomin 13 na jihar an ɗauke masu layukkan sadarwa a cigaba da yaƙar maharan daji da suka addabi yankin arewa maso yamma.
managarciya