Ƙungiyar Arewar Mu Duniyar Mu Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Matafiya A Jos Da Fataken Shanu A Aba
Daga Habu Rabeel, Gombe
Kungiyar arewar mu Duniyar mukungiya ce ta yan arewa dake da helkwata a garin Kaduna da aka kafa ta domin kare ‘yanci da martabar yan arewa a duk inda suke sannan suyi Magana da harshe daya.
Shugaban kungiyar na kasa lhaji Ibrahim Haruna Tukulma, yace a kungiyan ce sun yi Allah wadai da kisan da akayi wa yan arewa hudu a garin Filato da kuma yadda yan kudu suka kashe wasu Fataken shanu gami da hallaka musu shanun a lokacin da ake ganin komai zai dai dai ta.
Alhaji Haruna wanda har ila yau shi ne sarkin Hausawan Tukulma, yace kashe yan arewar da akayi a garin Jos zai mayar da hannun agogo baya domin an fara samun zaman lafiya amma sai gashi ana samun tashe-tashe sannan a kudancin Najeriya kuma wasu batagari suka halaka Fataken shanu suka kashe kuma kashe musu shanun su
A cewar sasuna kiran gwamnatin kasar nan da ta dauki mataki na gano wadanda suka aikata kisan domin a musu hukunci wanda hakan zai dan sanyaya zukatan yan arewa na hana su daukar fansa.
Ya kuma ce ba za su ce a dai na kai musu dabbobi ko kayan abinci acan kudancin amma dai kan kungiyar su na kira ga hukumomi da cewa su tashi tsaye dan shawo ka irin wannan rikici.
Alhaji Haruna, ya shawarci yan arewa da cewa su tsakaita wasu aikace-aikacen Su na safarar kayayyakin abinci da Nama da suke kai wa kudancin Najeriya domin watakila jin zafin an daina kai musu kayan zai sa su dai na kashe mutane.
Daga nan sai ya yi amfani da damar ya kirayi sarakunan arewa da ma gwamnonin arewa akan cewa su tashi tsaye wajen ganin samu dai daitu an daina kashe yan arewar mu saboda wata manufa ta daban da son zuciya.
managarciya