Wazirin Tambuwal Yaya Ga Gwamnan Sakkwato Ya Rasu
Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto.
Allah yawa Alhaji Muhammad Bello Wazirin Tambuwal rasuwa a jiya Talata, bayan ya jima yana jinya, inda aka yi Janazarsa, kamar yadda shari'ar musulunci ta tanada, a Fadar Uban kasar Tambuwal, a garin Tambuwal.
Margayi wazirin Wanda yake Yaya ne ga maigirma Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya shafe shekara 37 yana matsayin Wazirin Tambuwal bayan ya gaji Margayi Alh Umar Waziri Usmanu.
Garin na Tambuwal ya cika makil da manyan mutane daga sassan jihar Sokoto, kebbi zamfara da Abuja da sauran wurare daban daban. Sallah ta samu halartar Gwamnan Tambuwal, wakilin mai mai martba sarkin Musulmi, tsofaffin gwamnoni, malammai,sarakuna,yan siyasa, 'yan kasuwa, maaikatan Gwamnati, da sauran su.
managarciya