Kisan Hausawa a Edo:Inyamurai Sun Rufe Shaguna gudun kai hari a Sokoto

Kisan Hausawa a Edo:Inyamurai Sun Rufe Shaguna gudun kai hari a Sokoto


An shiga fargaba a jihar Sakoto sakamakon jita-jitar zanga-zangar da ake shirin yi da kuma zargin kai harin ramuwar gayya kan kisan Hausawa 16 da aka yi Edo. 
Idan ba a manta ba, an  rahoto cewa wasu bata gari sun tare motar fasinjoji a garin Uromi, jihar Edo, inda suka kashe mafarauta 16 da ke hanyar zuwa Kano. 
Wakilin jaridar Punch da ke Sokoto ya lura a ranar Juma’a cewa an rufe yawancin shagunan da baƙi ke gudanar da kasuwanci, musamman Inyamurai. 
An ce an rurrufe yawancin shagunan da ke cikin unguwannin da Inyamurai suka fi yawa birnin jihar, irin su Bello Way, Emir Yahya, Sahara da Aliyu Jodi. Wani mai shago da ya bayyana sunansa da Chinedu, ya ce tsoron kai masu harin ramuwar gayya ne ya sa ya rufe shagonsa, inda ya ce yana gudun ya yi asarar dukiyarsa. 
“Mun ji jita-jitar cewa wasu matasa za su yi zanga-zanga bayan sallar Juma’a, kuma hakan na iya kai wa ga kai harin ramuwar gayya, shi ya sa muka dauki matakin rufe shaguna. 
“Ba za mu jira abin ya faru ba kafin mu yi shiri, shi ya sa muka rufe shagunanmu." - Inji Chinedu.
Haka zalika, wani Inyamuri da ke sayar da tayar motoci a Unguwar Sahara ya ce tsoron masu fasa shaguna ne ya sa suka rufe nasu shagonsu. 
A bangarenta, rundunar ‘yan sanda ta Najeriya reshen jihar Sokoto ta tabbatar da cewa tana cikin shiri domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Mai magana da yawun rundunar, DSP Ahmed Rufai, yayin da yake magana da wakilin jaridar, ya ce an tura jami’an tsaro zuwa sassan birnin domin tabbatar da doka da oda. Sai dai wakilin jaridar ya tattaro cewa babu wani rahoton kai hari da aka samu har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto.