Gwamna Masari Ya Soke Bangar Siyasa Da Lika Fastoci A Katsina

Gwamna Masari Ya Soke Bangar Siyasa Da Lika Fastoci A Katsina
 

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya rattaba hannu a wata sabuwar doka a yunƙurin sa na magance rashin tsaro a jihar.

 

Yahaya Sirika, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al'adu na jihar, shi ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma'a a Katsina.

 
Sirika ya yi bayanin cewa gwamnan ya yi amfani ne da sashi na 176(2) na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa na 1999 da  ya baiwa gwamnan jiha ikon yin doka a kan kansa.
 
A cewar sa, dokar, wacce ta fara aiki tun 1 ga watan Janairu, ta yamma dukkanin wani nau'i na dabancin siyasa da aikata wasu Laifuka makamantan hakan.
 
Kwamishinan ya ƙara da cewa dokar ta kuma hana manna fastocin siyasa a rawul-rawul, gine-ginen gwamnati, ofisoshi da sauran guraren jama'a a jihar.
 
Ya ce dokar ta hana duk wani taro na ƴan baranda siyasa da su ka haɗa da Bacha, Ƙauraye, koma wanne irin suna a ke kiransu, da zai razana al'umma a jihar.
 
Sirika ya yi gargaɗi cewa duk wanda ya saɓa dokar za a kama da kaifin karya sashe na 114 na dokar 'penal code' ta jihar.
Duk masu sharhi kan lamurran yau da kullum na kallon dokar ba za ta yi wani tasiri ba domin lokacin siyasa ne kuma a Nijeriya wadan nan abubuwan suna cikin gishirin dimukuradiyya.
Da yawan mutane a jihar sun zuba ido su ga yanda za ta kaya in aka fara gudanar da yekuwar zabe gadan-gadan don tunkarar 2023.