Ƙungiyar Anchor Ta Shirya Tàron Wayar Da Kan Matasa Muhimmancin Mallakar Katin Zaɓe A Neja

Ƙungiyar Anchor Ta Shirya Tàron Wayar Da Kan Matasa Muhimmancin Mallakar Katin Zaɓe A Neja
Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna.
Kungiyar hadin kai da wayar da kan jama'a Anchor Mind Initiative Movement da ke karamar hukumar Rafi ta shirya taron wayar da kan matasa muhimmancin mallakar katin zabe dan fuskantar babban zabe 2023.
Da yake jawabi, yayin bude taron, shugaban kungiyar Malam Musa Usman Algummawy, yace sun shirya wannan taron ne dan wayar da kan yan uwansa matasa muhimmancin mallakar katin zabe duba da irin nisar da aka yiwa yankin wajen tururuwar matasa a wasu yannkunan, wanda idan ka duba an bar matasan mu a baya.
Karamar hukumar Rafi, na daya daga cikin kananan hukumomin da suka samu koma baya sakamakon tarwatsewar jama'ar yankunan karkara na hare-haren yan bindiga. Mun cewar bai yiwuwa jama'ar da yan bindiga suka raba da muhallansu ka ce su koma matsugunnan su dan mallakar katin zabe, saboda kafin lokaci ya kure ya kamata a inda suke tsugunne yanzu su tabbatar sun sabunta katinsu, yaran da ba su mallaki katin ba a baya ba saboda shekarun su bai kai ba da yanzu sun cika shekarun jefa kuri'a su tabbatar su ma sun tafi cibiyoyin zabe da aka tanada dan su mallaki na su katin zaben.
Yau mun yi hadin guiwa da kungiyoyi takwas a wannan karamar hukumar, dan gayyato masana su yi mana karin haske kan alfanu, da hanyoyin da ya kamata matasan mu su bi wajen mallakar katin. 
A baya yan siyasa na anfani da matasan mu wajen bangar siyasa dan cin zabe wanda da an kai ga nasara ba wani ribar da hakan ke haifarwa, a wannan karon mun kuduri aniyar tsaftace siyasar mu ta hanyar wayar da kan matasan mu mata da maza wajen zaben mutanen da muke tsammanin zasu ba mu wakilci mai inganci da zai kawo mana karshen wannan matsalar na tsaro da ya addabi yankin mu.
Anchor Mind ba jam'iyyar siyasa ba ce, ba kuma wani dan siyasar da rike da mu, mun kafa wannan kungiyar ne dan ceto kasar Rafi daga mawuyacin halin rashin tsaro da muke fuskanta, saboda haka ba za mu yi kasa a guiwa ba wajen cigaba da wannan namijin aikin wayar da kan musamman na ganin an zabo mutane masu nagarta a zaben 2023, dan kaucewa siyasar ubangida, rashin mutunci da wulakanta zamantakewar jama'a.
Musa Usman ya yi kira ga yan siyasa musamman masu yunkurin ganin sai sun hau mulki da karfi, da su guji shirya abubuwan da zai cigaba da yin kafar ungulu ga zaman lafiyar al'ummar Rafi ke muradin gani.
Yanzu dai haka kauyuka da dama a cikin gundumomin karamar hukumar Rafi ke gudun hijira sakamakon hare-haren yan ta'adda da ya kai daidaita al'ummar yankin wadanda har yanzu ba su San makomarsu.
Taron dai ta gudana ne babban dakin taro na tunawa da tsohon shugaban karamar hukumar, da ya samu halarta daliban manyan makarantu ciki da wajen jihar, da shugabannan addininai da kungiyoyi da dama na karamar hukumar Rafi.