Jam'iyar PRP Ta Fice Daga Takarar Kujerar Gwamna Sa'o'i 48 Kafin Soma Zaɓe A Jihar Osun
Daga Jabir Ridwan.
Ana kasa da Sa'o'i 48 asoma Zabe a jahar osun jam'iyar PRP Mai Alamar Makulli ta bayyana cewa ta janye daga takarar kujerar gwamna a jahar.
Sakataren jam'iyar na kasa Babatunde Alli shine ya bayyana wannan mataki da jam'iyar ta dauka a ranar Alhamis.
Gidan Talabijin na channels ya ruwaito cewa Jam'iyar PRP acikin wani bayani tace "biyo bayan wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyar a don haka jam'iyar ta lura dacewa akwai wasu dabi'u maras kyau da Dan takarar gwamnan karkashin inuwar jam'iyar ke nunawa Mr Ayowole Olubusuyi Adedeji tun daga yanda zaben fitarda gwani yagudana na jahohi har ma da na kasa Baki daya.
Bayanin yakara dacewa la'akari da wannan ne kwamitin masu ruwa da tsaki na jam'iyar yakai matsaya domin janyewa daga zaben Wanda aka tsara zai gudana a 16 ga Watan Yuli 2022.
Bayaga janyewa daga zaben hakama jam'iyar tace zata nada wani kwamitin ladabtarwa domin gudanar da bincike akan Dan takarar gwamnan wato Adedeji.
Kwamitin dai ana San ran ya gudanarda bincike kan abubuwa ukku da ake zargin Dan takarar dasuka hada da kasancewar Dan takarar a kasashen waje na tsawon lokaci tun daga ranar da yasamu nasarar tsayawa takarar gwamna a jam'iyar, inda aka bayyana cewa ana sauran makonni biyu da zaben sannan Dan takarar yadawo Wanda yahana ma jam'iyar damar gudanarda yekuwa da wayarda Kai kamar yadda Yakamata.
Sauran zarge zargen sun hada da na almundahanar kudade masu yawa da nufin gudanarda yekuwa Amma Kuma Hakan Bata kasance ba, sai Kuma zargin sa da cefanar da jam'iyar a raayin kanshi da sauran su.
Gidan talabijin na channels ya ruwaito cewa akan haka jam'iyar tayi kira ga daukacin magoya bayanta da su cigaba da baiwa jam'iyar hadin Kai da goyon Baya domin lashe zabukan shekarar 2023 Mai zuwa inda tace ita Kam zaben jahar osun iyakacinta kallo.
managarciya